Connect with us

News

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana dalilinsa na yin kira ga al’ummar jiharsa da su nemi makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Published

on

FB IMG 16408578321238972
Spread the love

..

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a Katsina wanda aka yaɗa kai tsaye ta kafar Facebook, ya ce dole ne al’umma su tashi tsaye domin babu isassun jami’an tsaron da za su kare su.

Masari ya rika amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin wannan taro, kuma cikin tambayoyin da aka masa har da wadanda suka shafi harkokin tsaro.

Ya yi iƙirarin cewa an samu sauƙi a jihar Katsina duk da cewa abubuwa sun tsananta a Jihar Sokoto cikin kananan hukumomi guda biyu.

Advertisement

TALLA

Gwamnan wanda a baya yake ɗa’awar sulhu da ƴan bindiga kafin ya yi watsi da manufar, ya ce ‘yan sandan da ke jiharsa ba su kai 3,000 ba, yana mai cewa gwamnati za ta taimaka wa masu son mallakar makaman don taimaka wa harkar tsaro.

“Harkar tsaron nan ta kowa da kowa ce babu bambancin siyasa – abin da mutane ya kamata su sani shi ne a Katsina ba ka da ‘yan sanda 3,000…saboda haka muke kira ga duk wanda zai iya ya nemi makami ya kare kan sa da iyalansa,” in ji Gwamna Masari.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa: “Shari’ar Musulunci ma ta yarda mutum ya kare kan sa da dukiyarsa da iyalansa. Idan ka mutu kana ƙoƙarin kare kanka ka yi shahada. Abin baƙin ciki ma shi ne ta yaya ‘yan fashi za su samu bindiga amma mutanen kirki ba su da ita da za su kare kansu da iyalansu

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *