News
LABARAIFact Check: Alhaji Bashir Tofa na nan da ransa
Iyalan Alhaji Bashir Usman Tofa sun musanta labarin rasuwarsa da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta.
Ɗaya daga cikin makusantansa Alhaji Ahmed Na’abba ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Na’abba ya ce, biki aka yi a kusa da gidansa shi ne aka ga tarin motocin bayan sallar magriba, daga nan ne kuma wasu suka fara yaɗa wannan jita-jita.
Freedom Radio ta yi tattaki har zuwa gidan Alhaji Bashir Tofa da ke unguwar Gandun Albasa ta kuma iske cewa babu wani abu da ya sauya na alamun yin rasuwa.
Sai dai Freedom Radio ta lura da yadda aka sanya jami’an tsaron suna bincike a titin unguwar Gandun da ma wasu tituna a birnin Kano.
Hakan kuma baya rasa nasaba da ƙoƙarin jami’an tsaro na daƙile masu son wuce gona da iri da sunan murnar sabuwar shekara.
A nata gamayyar ƙungiyoyin Arewa na CNG sun yi martani ga masu yaɗa jita-jita ta bakin jami’inta Malam Ali Shettima wanda ya ce babu ƙamshin gaskiya ga labarin rasuwar.
Alhaji Bashir Tofa shi ne uban ƙungiyar ta CNG