News
Za a hana ɗalibai ƴan luwaɗi da maɗigo zuwa makarantun kwana a Kenya
Ministan ilimi na ƙasar Kenya, George Magoha ya ce akwai buƙatar a haramta wa duka ɗalibai ƴan luwaɗi da ƴan maɗigo zuwa makarantun kwana a ƙasar.
Ministan ya ce za a mayar da ɗaliban zuwa makarantun jeka-ka-dawo domin gudun kada su durmiyar da sauran ɗalibai.
Sai dai tuni ƙungiyoyi masu zaman kansu suka ce za su ƙalubalanci duk wani yunƙuri na take haƙƙin ƴan luwaɗi da maɗigo.
Ana hukunta waɗanda aka samu da laifin luwaɗi a Kenya da zaman gidan yari na shekara 14.
Mista Magoha dai ya kuma yi kira da a gudanar da gwajin miyagun ƙwayoyi ga ɗalibai idan aka dawo hutun sabuwar shekara.