News
Babu Maganar komawa ta APC — Kwankwaso
Daga kabiru basiru fulatan
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bashi da wani shiri na barin jam’iyyar sa ta PDP Zuwa Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya.
Sanata Kwankwaso ya baiyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon DW da ke Ƙasar Jamus.
DW ya rawaito Sanata Kwankwaso ya na cewa a yanzu dai bashi da wata niyya ta barin jam’iyyar PDP Zuwa APC, kamar yadda a ke ta jita-jitar zai bar jam’iyyar saboda rashin Ylyi da shi da ba a yi a jam’iyyar.
“Maganar sauya sheƙa babu ita a yanzu ɗin nan. Ba na magana da wasu mutane kan cewar kan koma APC” inji Kwankwaso.
Jita-jita ta yi ƙarfi cewa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa APC kuma zai sulhunta da abokin burminsa a siyasa, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje bayan da gwamnan ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar ƙanin sa, Inuwa Kwankwaso.
Sai dai kuma a makon nan da mu ke ciki, sai gwamnatin Ganduje ta yi wa Kwankwason raddi kan kalaman da ya yi cewa gwamnan bai ci zaɓe ba a shekarar 2019.
Idan za’a iya tunawa an fara raderadi Kwankwaso da Ganduje zasu yi Sulhu ne tun bayan da Gwamna Ganduje ya Kaiwa Sanata Kwankwason Ziyarar ta’aziyyar kaninsa da ya rasu a kwanakin baya.