Mutum goma sha daya sun mutu a yankin Bugesera da ke kudu maso gabashin Rwanda tun daga ranar Kirsimeti bayan sun sha wata burkutu da aka yi da ayaba, a cewar Hukumar Bincike ta kasar.
Rahotanni sun ce an kwantar da mutum hudu a asibiti domin yi musu magani.
Hukumar kula da Abinci da Magunguna ta Rwanda ta ce an gano sinadarin methanol mai yawan gaske a cikin gawarwakin mutanen da suka sha burkutum, kuma ana tunanin hakan ne ya haddasa mutuwarsu.
An kama mutum biyar, ciki har da mutumin da ke da gidan sayar da burkutun.
Hukumar ta kara da cewa an bude gidan sayar da burkutun ba tare da lasisi ba, kuma yanzu haka an rufe shi.
An kaddamar da kamfe na rufe dukkan shagunan sayar da burkutun da ba su da lasisi.