News
Jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Sudan
Jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Sudan
Jami’an tsaron Sudan sun yi amfani da hayaki mai sa-kwalla wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi fitar-dango, suna rera wake-waken tofin-alatsine ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar. Wannan na zuwa kwanaki kalilan da Firaministan kasar, Abdalla Hamdok ya yi murabus daga mukaminsa.
A cikin wake-wakensu, masu zanga-zangar a birnin Khartoum sun yi ta fadin “Ba sa son mukin soji, suna masu kira da a gaggauta rusa majalisar mulkin sojin kasar karkashin shugabancin Janar Abdel Fatah al-Burhan wanda ya jagoranci juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata, matakin da ya sukurkuta shirin maida a mulki ga farar hula zalla.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun datse hanyoyin da suka ratsa zuwa fadar shugaban kasa da kuma shalkwatan sojoji kamar yadda shaidu suka tabbatar.
Jami’an tsaron sun cilla borkonon tsohuwa a kusa da fadar shugaban kasa da kuma wasu wurare da masu zanga-zangar suka yi cincirindo a sassan kasar.
Ba ya ga Khartoum, an samu cikowar dubban masu boren a biranen Omdurman da Nyala da ke Kudancin Darfur.
A makon jiya ne, Firaminista Abdalla Hamdokn ya yi murabus, makwanni shida da Janar al-Burhan ya sake mayar da shi kan karaga.
A jawabin da ya gabatar, Hamdok ya ce, kasar ta Sudan ta tsunduma cikin wani irin bala’in da ke matukar barazana game da makomarta.