News
2023: Ƙungiyoyin Arewa sun kaɗa kugen goyon bayan Osibanjo a matsayin shugaban ƙasa
Daga kabiru basiru fulatan
Gamaiyar Ƙungiyoyi a yankin Arewa sun baiyana goyon bayan su ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osibanjo a matsayin ɗan takarar su a zaɓen 2023.
Gamaiyar ƙungiyoyin sun baiyana matsayar ta su ne a jiya Laraba a wata sanarwar bayan taron da su ka yi a Kaduna a kan damawa da ƴan Arewa a harkokin siyasa da kuma sauyin mulki.
Sanarwar ta samu da hannu na haɗin gwiwa da ga Daniel Shawulu na Arewa Consensus Assembly, Suleman Makama, National Partnership campaign project da kuma Khalid Mohammed Joint Participation for Development Initiative.
Ƙungiyoyin sun ce bayan tattaunawa da tuntuba ta tsanaki, sun gano ce Osibanjo ne amsa a 2023.
“bayan tattaunawa da tuntuba da tunani na tsanaki, ba wai ra’ayin siyasa ba, mun gano cewa Osibanjo ne amsa, musamman ga mu ƴan Arewa.
“Shine amsa ga matsalar daidaito da kuma sauyin mulki, nagarta da kuma kwarewa kamar yadda taron ya fahimta,”