News
HASASHE: Za a samu zaman lafiya da haɓɓakar tattalin arziki a Nijeriya a 2022 — Masani
Daga kabiru basiru fulatan
Masani a fannin halaiyar ɗan’adam, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya yi hasashen cewa za a samu zaman lafiya a Nijeriya da kuma haɓɓakar tattalin arziki a sabuwar shekarar 2022.
Farfesa Malumfashi ya yi wannan hasashe ne a shirin Barka da Hantsi na Gidan Rediyon Freedom a Kano, da gidan jaridar indaranka ta saurara a yau Juma’a.
A cewar Farfesa Malumfashi, wanda Malami ne a Sashen Koya Ilimin Halaiyar Ɗan’adam a Jami’ar Bayero Kano, BUK, za a samu haɓɓakar tattalin arziki ne domin a wannan shekarar ne za a fara yaƙin neman zaɓen shekara ta 2023.
Ya ce a yayin yaƙin neman zaɓen, ƴan siyasa za su saki kuɗaɗe, waɗanda su ke kan madafun iko kuma za su yi aiyukan ci gaba, domin su samu goyon bayan al’umma.
Farfesan ya ƙara da cewa a yayin neman zaɓen, za a samu zaman lafiya sabo da talauci zai ragu sakamakon zagayawar kuɗaɗe cikin al’umma.
Ya kuma ƙara da cewa matasa za su zama sun samu abin yi, sakamakon yawon kamfe da za su riƙa zuwa, wanda zai ɗauke hankalin su da tunanin su da ga aikata laifuka da kuma shan ƙwayoyi, sannan ga kuɗaɗe su na samu.
Farfesan ya yi kira ga ƴan siyasa, musamman waɗanda su ke kan madafun iko, da su yi duba da wannan yanayin da a ke hasashen za a shiga su kuma yi amfani da dabarun a shekaru na gaba domin samar da zaman lafiya da haɓɓakar arziki a ƙasar.
Ya kuma ƙara da cewa, ba ma Nijeriya kaɗai ba, a duniya ma baki daya za a samu haɓɓakar tattalin arziƙi a wannan shekara ta 2022 kamar yadda cibiyoyin hada-hadar tattalin arziki da dama a faɗin duniya su ka yi hasashe.