News
Wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya sun gurfanar da kwamatin shugabancin jam’iyyar na riƙo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe a gaban Babbar Kotun Abuja.

Daga Muhammad zahraddin
Wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya sun gurfanar da kwamatin shugabancin jam’iyyar na riƙo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe a gaban Babbar Kotun Abuja.
Suleiman Usman da Muhammed Shehu da Samaila Isahaka da Idris Isah da Audu Emmanuel na neman kotun ta dakatar da gwamnan da kwamatinsa gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa a watan Fabarairu, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Cikin ƙarar da suka shigar mai kwanan watan 4 ga Janairun 2022, sun gurfanar da jam’iyyar APC da shugbanta da kuma hukumar zaɓe ta INEC.
Masu shigar da ƙarar ta bakin lauyansu, Olusola Ojo, sun buƙaci a dakatar da taron ne saboda, a cewarsu, har yanzu wasu daga cikin tarukan a matakin jihohi ba su kammalu ba.
Sun nemi kotun ta amsa tambaya biyar sannan ta ba da umarni takwas.
Yayin taron na ƙasa ne APC za ta zaɓi shugabanta na ƙasa kamar yadda aka yi a matakin jihohi da mazaɓu, abin da har yanzu wasu ke taƙaddama a kai.