Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Haaland, Fernandes, Morata, Kepa, Kamara, Danilo
Daga Yasir sani Abdullah
Ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland na ganin Manchester City za ta yi kokarin daukarsa bayan da Manchester United ta janye daga jerin kungiyoyin da ke son raba mai shekara 21 da Jamus. (Mario Cortegana via Express)
Idan kuwa Barcelona ta gaza daukan Haaland a karshen wannan kakar wasan, to Bruno Fernandes dan wasan tsakiya na Manchester United mai shekara 27 ne wanda za su fi mayar da hankali kansa. (El Nacional, via Mail)
Dan wasan Sfaniya Alvaro Morata na daf da yanke kauna da Juventus saboda ya koma Barcelona, amma kocinsa Massimiliano Allegri ya ki amincewa da bukatar dan wasan mai shekara 29, amma zai iya sauya ra’ayi har sai bayan ya sami wanda zai maye gurbinsa. (AS – in Spanish)
Lazio na sha’awar mai tsaron bayan Chelsea Kepa Arrizabalaga, amma albashin dan wasan mai shekara 27 dan Sfaniya na fam 170,000 a kowane mako ya kasance babban cikas. (The Athletic – subscription required)
Dan wasan bayan Marseille Boubacar Kamara na son duk wata kungiya mai son raba shi da kungiyar ta biya shi fam 150,000 a kowane mako. Ya bayyana haka ne bayan da West Ham da Newcastle suka fara nuna sha’awar daukan dan Faransan mai shekara 22. (Sun).
Barcelona na son Adama Traore, dan wasan Wolves mai shekara 25 idan dan wasanta Ousmane Dembele mai shekara 24 ya yanke kauna da ita. (Diario Sport – in Spanish)
Birmingham City na daf da dauke Amad Diallo, dan wasan Manchester United mai shekara 19 amma a matsayin dan aro ba na din-din-din ba. (Mirror)
Ƙungoyin Aston Villa, Crystal Palace, Newcastle da West Ham na son Bamba Dieng dan wasa gaba mai shekara 21 daga Marseille. (La Provence, via Sport Witness)
Mataimakin shugaban Barcelona Rafa Yuste ya ce kungiyar na bukatar sayar da karin ƴan wasa kafin Ferran Torres, dan wasan gaba mai shekara 21 zai iya komawa Camp Nou daga Manchester City. (Barca Blaugranes)