Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Haaland, Martial, Rashford, Wijnaldum, Coman, Ndombele da Nketiah

Published

on

114251310 hi062050896
Spread the love

Daga Usman Abdulahi jibirin Nguru Yobe

Borussia Dortmund na shirin ganawa da wakilan dan wasan Norway Erling Braut Haaland a mako mai zuwa a yayin da suke kokarin sanin tsare-tsaren dan wasan mai shekara 21 game da makomarsa. (Marca)

Sevilla ta sassauta sha’awarta game da daukar dan wasan Faransa Anthony Martial saboda ba za ta iya cika sharudan da Manchester United ta sanya mata ba na karbar aron dan wasan mai shekara 26. (Marca)

Advertisement

Ana rade-radin cewa dan wasan tsakiya na Paris St-Germain Georginio Wijnaldum zai tafi Newcastle United amma dan kasar Netherland mai shekara 31 ba ya sha’awar komawa tsohuwar kungiyarsa. (Football Insider)

Tsohon kocin Tottenham Jose Mourinho ya tuntubi dan wasan tsakiyar Spurs Tanguy Ndombele a yunkurin rarrashin dan wasan mai shekara 25 dan kasar Faransa ya same shi a Roma, yayin da kungiyar ta kasar Italiya take son karbar aronsa da kuma zabin sayensa. (Telefoot, via Mail)

Ana sa ran dan wasan gaba Marcus Rashford, mai shekara 24, zai tattauna da Manchester United game da sabunta kwangilarsa, inda ake tunanin za su soma tattaunawar kafin karshen kakar wasa ta bana. (Mail)

Advertisement

Crystal Palace tana tattaunawa domin dauko dan wasan Ingila Eddie Nketiah daga Arsenal, a yayin da kwangilar dan kwallon mai shekara 22 take shirin karewa a bazara, (Times – subscription required)

Matashin dan wasan Arsenal dan kasar Ingila Folarin Balogun, mai shekara 20, yana shirin tafiya Middlesbrough domin zaman aro na ragowar kakar wasa ta bana. (Sky Sports)

Brighton da Newcastle United na kokarin daukar dan kasar Argentina Marcos Senesi, mai shekara 24, daga kungiyar kasar Netherlands Feyenoord. (Football Insider)

Advertisement

Tottenham tana son daukar dan wasan baya da na tsakiya da kuma na gaba idan aka bude kasuwar musayar ‘yan kwallo ta watan Janairu bayan an tattauna tsakanin kocin kungiyar Antonio Conte, da shugabanta Daniel Levy da kuma manajan darakta kan kwallon kafarta Fabio Paratici. (Telegraph – subscription required)

Dan wasan Faransa Kingsley Coman, mai shekara 25, yana dab da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a Bayern Munich. (Goal)

Chelsea na duba yiwuwar yin kiranye ga dan wasan Ingila Dujon Sterling, mai shekara 22, daga zaman aron da ya kwashe kakar wasa daya yana yi a Blackpool sai dai ba za ta iya yin hakan ba bayan 14 ga watan Janairu. (Football League World)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *