Business
Dare daya ALLAH Kan yi bature , Kudin Crypto yasa talaka ya Shiga sahun Masu kudin Duniya inda tuni ya tsrewa Mai kudin Africa Aliko Dangote.
Daga Yasir sani Abdullah
Crypto ta sa Zhao ya zama mutum na 15 a masu kudin Duniya, ya ribanya Dangote sau .
Rahotanni sun nuna cewa Changpeng Zhao shi ne na 15 a sahun manyan masu kudin Duniya a 2022 Shugaban kamfanin Binance ya mallaki kusan Dala biliyan 100 a sakamakon gawurtar da Crypto .
Arzukin Zhao kusan ya nunka na Aliko Dangote hudu a hali yanzu, Dangote ya mallaki kusan $20bn.
Shugaban kamfanin Binance, Changpeng Zhao mai shekara 44 da haihuwa, ya shiga sahun gawurtattun masu kudin da ake ji da su a fadin Duniya.
Wani rahoto da Intel Region ta fitar a makon nan ya nuna Changpeng Zhao ya na cikin manyan attajirai 15 na Duniya, mallaki sama da Dala biliyan 96.
Jaridar tace dukiyar shugaban kamfanin na Binance a wancan lokaci bai wuce Dala miliyan 15 ba.
Aliko Dangote shi ne mai kudin Afrika (har gobe), a wancan lokaci Changpeng Zhao ma’aikaci ne da yake karbar albashi.
Rahoton da Bloomberg ta fitar a karshe ya nuna cewa babban mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya na da kusan $20bn, 20% na abin da Zhao yake da shi a yau.
Yanzu maganar da ake yi, Zhao ya sha gaban Mukesh Ambani a jerin masu kudin Duniya, ya kama hanyar kamo kafar Mark Zuckerberg da Larry Page.