News
Na so a ce na rayu da iyayena – Janar IBB
Daga kabiru basiru fulatan
A wata hira da wani gidan talabijin suka gabatar da tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda aka fi sani da IBB, a shirin AriseTV, janar ɗin ya bayyana cewa ya so a ce ya rayu da iyayensa sun ga irin yadda ya girma da cigaban da ya samu a rayuwa.
IBB ya bayyana haka ne a lokacin da aka tambaye ko zai iya tuna wani mai muhimmanci da ya so a ce ya faru a rayuwarsa, amma bai faru ba, ko kuma wani abu da bai so a ce ya faru ba, amma ya faru?
Daga nan ne IBBn ya bayyana cewa: “na so a ce na rayu da iyayena, ko da ɗaya daga cikinsu ko su biyun domin su ga yadda na zama soja. To amma na rasa dukkaninsu tun ina ɗan shekaru 14.
Ko da aka tambaye shi, shin hakan ya yi tasiri a wajen mu’amalar da al’umma? Shugaban ya bayyana cewa shi dai ya so a ce yadda suka so ya zama mutumin kirki suka dinga yi masa kyakkyawan fata, ya so a ce sun rayu sun ga girmansa, to amma Allah bai ƙaddara hakan ba.
A cikin hirar da jaridar indaranka ta bibiya, hirar shugaban ta nuna girman iyaye da ƙimarsu, ta yadda shugaban soja da ya kai shekaru sama da 80, kuma ya rasa iyayensa tun kusan shekaru 70, amma bai manta da su ba. Lallai iyaye suna da muhimmancin da ya kamata duk wanda yake da nasa a raye, to ya kamata ya girmama su don dole wata rana za a rabu.