News
An damƙe kwamandan vigilante kan zargin ganawa ƴar sanda azaba a Anambra

Daga kabiru basiru fulatan
Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Anambra, Echeng Echeng ya ce rundunar sa ta cafke kwamandan ƴan vigilante na jihar a kan zargin ganawa wata ƴar sanda azaba.
An cafke kwamandan ne, wanda a ka sakaya sunansa, bayan da ya azabtar da ƴar sanadan a Ƙaramar Hukumar Awuda Nnobi in Idemili ta Kudu a ranar 12 ga watan Janairu.
Kakakin Rundunar a jihar, Tochukwu Ikenga, a wata sanarwa da ya fitar, ya sanar da cewa kwamandan na hannun ƴan sanda a tsare.
Ikenga ya yi bayanin cewa wani fefen bidiyo da ya yi ta yawo a yanar gizo, inda a ka nuna jami’an vigilante ɗin su na azabtar da ƴar sandar a ofishin su ne ya sanya Kwamishinan Ƴan Sandan jihar ya bada umarnin a kamo kwamandan.
Kwamishinan ya kuma bada umarnin bincike a kan lamarin.
“Rundunar ta suffanta lamarin a matsayin tsoro, inda ya ƙara da cewa rundunar a shirye ta ke da ta kare mata wajen cin zarafi da a ke yi musu, ko da ma ba jami’ar tsaro ba ce,”
Kakakin ya kuma godewa al’umma sakamakon alla-wadai da su ka yi da abin da ya faru.