News
Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin da zai duba lamarin karuwai da masu shaye-shaye
Daga usmaU Abdullah jibirin
Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kafa wani kwamiti da zai shiga lamarin fandararru da suka hada da masu tu’ammali da kayan shaye-shaye da karuwai da nufin gyaran halin su.
Kwamitin, mai mutane 15 karkashin jagorancin Sarkin Fadan Katsina, Alhaji Samaila Damale yana da mambobi daga jami’an gwamnati, shugabannin gargajiya, malaman addini da kuma shugabannin fararen hula.
Da yake zantawa da ‘yan jarida jim kadan bayan gama wata ganawar sirri da Gwamnan jihar Katsina a cikin satin da ya gabata, Alhaji
Shima da yake ansa tambayoyin manema labarai, mai ba Gwamna shawara akan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Katsina wanda shi ya jagoranci kwamitin zuwa wurin Gwamnan, yace gwamnati ta lura laifuka da dama na da alaka da fandarewar wasu a cikin al’umma.
Ibrahim Katsina ya cigaba da cewa wannan ne ma ya sa gwamnatin ta sha alwashin shiga gaba domin gyaran halin fandararrun day nufin samun sauki matsalar tsaron da ta addabi jihar