News
NDLEA ta kama kwayar Tramadol miliyan 1.5 da za a kai Kano
Daga muhammad muhammad zahraddin INDARANKA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama ƙwayar Tramadol miliyan daya da dubu dari biyar da za a kai jihohin Kano da Kebbi.
An kama ƙwayoyin ne a filin jirgin saman Legas, da tashar jiragen ruwa ta Apapa.
NDLA ta ce ta kuma gano wasu ƙwayoyi masu yawa da suka hadar da Diazepam, da Bromazepam, da allurar Pentazocine da suma aka so shigarwa jihar Kano
Hukumar ta kuma ce ta kama makamai, da harsasai da dama daga wajen wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar Plateau.
Ga bidiyon kayan da aka ƙwace nan a ƙasa don ku kalla.