Firaiministar New Zealand, Jacinda Ardern, ta ce yankin Tonga ya daidaice sakamakon aman wuta da duwatsu suka yi ga, sai dai har yanzu babu wani da hukumomi suka sanar da mutuwarsa.
Sai dai fannin sadarwa na da matukar wuya, inda wayar tarho ta girke ba sa aiki, kuma Mis Arden ta ce har yanzu ba ta yi magana da takwaranta na Tonga ba.
Dakta Marco Brenna na jami’ar Otago ya ce masarautar Tonga ta na da irin wadannan duwatsu masu aman wutar, a tsakiyar teku suke, don haka su na tsuburan masu nisa, don haka ne ba a cika sanya ido akan abin da ka je ya zo ba, misali New Zealand na sanya ido sosai kan na ta. Wasu hotuna da aka yada sun nuna yadda wani bangare na dutsen Hunga Tonga-Hunga Haʻapai mai aman wuta da ke cikin ruwa ya bace babu alamunsa.