News
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da harin fatattakar barayin daji a Ne
Daga KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar wani gagarumin aikin sojoji a jihar Neja, wadda ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga ‘yan fashin daji da kuma gyauron ‘yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram da ta ce suna tserewa daga yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Mallam Garba Shehu ya ce a wani umarni da ya bai wa hedikwatar tsaro kwanaki ƙalilan da suka wuce, Muhammadu Buhari ya buƙaci sojoji su mai da martani mai ƙarfi ga batutuwan kashe-kashe da sace mutane dona neman fansa a jihar ta Neja.
A saƙonsa ga gwamnati da al’ummar Neja, Shugaba Buhari ya kuma jajenta musu kan matsalolin tsaro na baya-bayan nan da aka fuskanta.
Mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Mallam Garba Shehun, ya shaidawa BBC cewa manufar wannan da gagarumin aikin soja a jihar Nejan, shi ne matsalar tsaro da ‘yan fashin na daga cikin dalilan da ya sa gwamnati ta dauki matakin.
Malam Garba ya kara cewa: ”Bayanai sun nuna cewa ‘yan fashin daji da ake fatattaka daga jihohin Zamfara sun fara kwarara jihar Neja, gwamnatin jihar ta tabbatar hatta ‘yan Boko Haram sun ketaro tare da fakewa a dazukan da ke Neja.
Saboda haka wannan abu ya damu shugaban kasa, don haka ya bada umarni mai karfi aje dazukan a kuma fatattaki wadannan mutane. Kuma da yardar Allah za a ga abin da zai biyo bayan wannan gagarumin aiki.”
Garba Shehu ya ce tuni aka fara wannan aiki, domin daman nan ta ke shugaban kasa ya bada umarnin a fara, tuni mayaka da jirage na sama su fara wannan aiki.
Ya kara da cewa rashin layin wasar sadarwa n adaga cikin dalilan da bayanai bas a fitowa kan halin da ake ciki. Amma y ace ciukin kankanin lokaci shalkwatar tsaro ta Najeriya za ta fitar da bayanai kan yadda aikin ke gudana da kuma halin da ake ciki.
Jihar Neja ta jima ta na fuskantar matsaloli da dama, kama daga na ‘yan fashin daji, da masu garkuwa da mutane da kuma yakan Boko Haram da gwamnatiun jihar ta sanar da kwararsu.
Sai dai wani na ganin tuntuni ya kamata shugaba Buhari ya dauki wannan mataki, amma Malam Garba yace ana daukar matakan da suka dace tuntuni, yanzu ne dai aka kaddamar da gagarumin aiki kan hakan.
Matsalar tsaro na ci gaba da zama babban kalunbale, musamman a yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma, inda matsalar barayin daji da garkuwa da mutane ta ke kara ta’azzara baya ga matsalar mayakan Boko Haram da ISWAP.