Connect with us

News

Mun gano manyan aiyuka 460 da a ka maimaita su cikin kasafin kuɗi na 2022 — BudgIT

Published

on

Spread the love

Daga KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

Advertisement

BudgIT, ƙungiya mai zaman kan ta da ta ke bin diddigin kasafin kuɗi, ta baiyana cewa ta gano aiyuka 460 da a ka yi maimancin su a cikin kasafin kudi na 2022.

Iyanu Fatoba, Jami’in kula da Harkokin Sadarwa na BudgIT ne ya baiyana hakan a wata sanarwa.

A ranar 31 ga watan Disamba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kasafin kuɗi na naira tiriliyan 17.13 na 2022.

Advertisement

Sai dai kuma BudgIT ta gano naƙasu a cikin kundin kasafin kuɗin, inda ta ce aiyuka 460 da a ka sanya su sau biyu a cikin kundin ya kai kimanin naira biliyan 378.9.

BudgIT ta ce ta gano matsalar ne bayan ta bi diddigin manyan aiyuka 21,108 cikin kundin kasafin kuɗin da tuni shugaban ƙasa ya sanyawa hannu.

Ƙungiyar ta yi tuni cewa a kasafin kuɗin 2021 ma, manyan aiyuka 316 a ka maimaita bayan da Majalisun Wakilan ƙasar nan su ka sanya hannu.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa Hukumar Yaƙi da Cin-hanci ta ICPC ce ta gano aiyuka 257, sai kuma ita BudgIT ɗin ta gano 185 da a ka sanya sau biyu-biyu a kasafin kuɗin na 2021.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa da ya ke magana a kan gano aiyukan, Gabriel Okeowo, Daraktan Ƙasa na BudgIT, ya ce “wasu kurarai ne na gangan domin a yi almundahana”.

Ya kuma yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a ƙasar nan da su tashi tsaye wajen kwarmata wannan almundahanar domin tabbatar da cewa an yi wa ƴan ƙasa aiyuka ba wai son ran wasu tsirarun ƴan siyasa ba.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *