Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Martial, McGinn, Zapata, Barisic, Melo, Milinkovic-Savic
Usman Abdullahi Nguru Yobe
Dan wasan Faransa Anthony Martial mai shekara 26 na son barin Manchester United amma ba ya son komawa wata kungiuyar gasar firimiyar Ingila a matsayin dan aro. (Fabrizio Romano)
Manchester United na son dan wasan tsakiya na Aston Villa da Scotland John McGinn a karshen wannan kakar wasan. (Telegraph – subscription required)
Newcastle United sun mika tayin euro miliyan 30 ga Atalanta kan dan wasanta na gaba Duvan Zapata mai shekara 30. (Daily Record)
Dan wasan baya na Rangers Barisic mai shekara 29 ya tabbatar cewa wata kungiya ta tuntube shi bayan da aka bude kasuwar ‘yan wasa a farkon watan nan. Ana rade-radin Watford da Aston Villa na sha’awar sayensa. (Sky Sports)
Tattaunawar da Arsenal ke yi da Juventus kan bayar da aron dan wasa tsakiya Arthur Melo mai shekara 25 ta tsaya cik saboda Juve ba ta sami wanda zai maye gurbinsa ba. (Tuttomercatoweb, via Express)
Chelsea na iya samun saukin daukan Aurelien Tchouameni, dan wasan tsakiya mai shekara 21, inda a yanzu Manchester United ta fi mayar da hankalinta kan Amadou Haidara, dan wasan tsakiya mai shekara 23 na RB Liepzig. (football.london)
Diego Costa na son komawa Corinthians ta Brazil maimakon Arsenal, inda dan wasan mai shekara 33 zai iya hadewa da tsohon dan wasa Chelsea Willian. (Evening Standard)
Manchester United na kan gaba wajen riga Juventus da Inter Milan wajen sayen Sergej Milinkovic, dan wasan tsaliya kuma dan kasar Serbia mai shekara 26 daga Lazio kan feuro miliyan 80. (Il Messaggero via Sport Witness)