Wasu matasan musamman wadanda suka rungumi harkokin siyasa na ganin akwai rawar da ya kamata za su taka wajen ceto kasar daga tarwatsewa.
Najeriya kasa ce wadda Allah ya albarkata da arzikin kasa da jama’a masu hazaka musamman idan aka kwatanta da kasashen nahiyar Afirka.
Sai dai ci gaban kasar bai zamo abin madalla ba ga mafi yawan al’umomin kasar.
Da yawan jama’a na dora alhakin koma-bayan kasar ga dalilai mabambanta, da kuma hanyoyin da suke ganin za’a iya samun mafita.
Matasan musamman wadanda suka rungumi harkokin siyasa na da bayanai daban-daban akan koma bayan kasar da kuma mafita.
Ambasada Aliyu bin Abbas matashin jam’iyar PDP ne kuma mataimaki na musamman ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
“Idan na je wasu kasashe, idan na ga yadda suka ci gaba, wallahi na kan yi kwalla, kuma idan na duba, sai na ga Najeriya ta fi wadannan kasashen komai. Amma kuma Allah ya jarrabe mu da miyagun shuwagabanni.” In ji Abbas.
“Duk abin da ka ga ana yi, yana da alfanu ga mutane. Da APC ta zo, tattalin arzikin kasa da wasu abubuwa duk ya lalace, arzikin man da yake zuwa ya karye.” In ji matashi na jam’iyar APC, kuma shugaban matasan jam’iyar mai kula da yankin arewa maso yamma, Abubakar Sadeeq Sa’ad Fakai
To ko me masana kan cewa akan tabarbarewar lamurran kasar da dukan jama’a suka yi ittifaki akai? Farfesa Abubakar Abdullahi masani ne akan kimiyar siyasa.
“’Yan siyasa na wannan zamani sun yi kasa a gwiwa, kusan dukkansu gaba daya kusan sune guda, yau wannan ya koma wannan bangare, yau wancan ya koma can idan ya ga bukatunsu ba su biya ba.” In ji Farfesa Abdullahi.
To sai kuma matasan sun yi amannar cewa suna da rawar da zasu taka ga samar da ci gaba zamowar su manyan gobe.
“Dole ne mu fito mu yaki zalunci da ake yi da cin amanar kasa.” In ji Abbas.
Shi kuwa Sa’ad Fakai cewa ya yi, “wannan ya zama wajibi gare mu mu ja hankalin manyanmu, mu kasarmu da kasarmu a gaba.”
Masana na da ra’ayin cewa duk gudunmuwar da za’a bayar ga samar da ci gaban Najeriya, ginshikin ta dole ya zamo shugabanci kyakkyawa, naa gaskiya da adalci.