News
Poland ta shiga zango na biyar na yaɗuwar annobar korona

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Mataimakin Ministan Lafiya na Poland, Waldemar Kraska ya sanar da cewa ƙasar ta shiga zango na biyar na yaɗuwar annobar korona, inda ya baiyana cewa an samu sabbin waɗanda su ka kamu da cutar 10,445.
A wani shirin gidan talabijin na Polsat, Kraska ya ce “zango na biyar ya iso mana bakin kofar gidajen mu.”
“Yau fa sabbin waɗanda suka kamu 10,445 a ka samu. Idan mu ka kwatanta wannan adadin na wannan makon da na makonnin baya, za mu ga cewa a kwai ƙari na kashi 34 cikin ɗari. An ɗauki kwanaki a na samun ƙari mai yawa kuma.
Kraska ya ƙara da cewa a na fargabar za ci gaba da samun ƙaruwar yaɗuwar annobar nan da makonni biyu ko uku, in da ya ce nau’in cutar na Omicron ya fi na Delta.
Mataimakin Ministan ya nuna cewa da ga cikin mutanen da a ka gano su na ɗauke da cutar a jiya, 611 da ga ciki Omicron ce ta kama su.
Tun fara annobar korona, cutar ta kama mutum 4,313,036, inda 3,790,377 su ka warke, 102,305 su ka mutu sannan 420,354 ne adadin waɗanda ke ɗauke da ita a ƙasar.