Sports
Ivory Coast ta yi waje da Algeria mai rike da Afcon

Daga muhammad muhammad zahraddin
Mai rike da kofi, Algeria ta yi ban kwana da gasar kofin Afirka da ake yi a Kamaru, bayan da Ivory Coast ta doke ta 3-1 a Doula ranar Alhamis.
Algeria wadda ta buga karawar da fatan yin nasara ko ta kai zagaen gaba, an zura mata kwallo biyu a raga tun kan hutu ta hannun Franke Kessie da kuma Ibrahim Sangare.
Dan wasan da ke taka leda a Arsenal, Nicolas Pepe ne ya ci wa Ivory Coast na uku, kuma kyaftin Riyad Mahrez ya buga fenariti amma kwallo ya bugi turke.
Daga baya ne Algeria ta zare daya ta hannun Sofiane Bendebka, kuma da wannan sakamakon ta yi ban kwana da gasar bana a rukuni na biyar mai rike da kofin da ta lashe a 2019 a Masar. Tawagar da Djamel Belmadi ke jan ragama ta zama ta uku da ke rike da kofi aka yi waje da ita a Afcon daga gasa biyar baya da aka fafata.
Algeria mai rike da kofin ta shiga gasar da Kamaru ke karbar bakunci a matakin wadda ta yi wasa 34 a jere ba tare da an doke ta ba, wadda ta yi fatan tarar da tarihin Italia mai karawa 37 a jere ba a ci ta ba a duniya.
Algeria ta fara wasan farko a cikin rukuni da tashi 0-0 da Saliyo, sannan ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Equatorial Guinea – ta kuma bar gasar bana da maki daya bayan fafatawa uku.
Ivory Coast ce ta zama kan gaba a rukunin, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu da Masar ranar Laraba 26 ga watan Janairu da za su kece raini a Doula.