Connect with us

News

Miji ya yi kisa bisa zargin kwartanci a kan matarsa a Kano

Published

on

FB IMG 16426817275562670
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Kotun Majistire mai lamba 29 da ke Jihar Kano ta bada umarnin ci gaba da tsare wani miji, Musa Yakubu, a gidan yari bisa zargin kashe wani da ya ke zargin ya na neman matarsa.

Tun da fari, a na zargin Yakubu da kashe Usman Tambaya, bayan da matar sa ta faɗa masa cewa a wasu lokuta a baya ya yi yunƙurin haike mata.

Jin haka, sai kishi ya tunzura Yakubu, inda ya je har gidan Tambaya, ya sassare shi da gatari har sai da ya ce ga garinku nan.

Advertisement

Tuni dai ƴan sanda su ka cafke Yakubu kuma a ka gurfanar da shi a kotun Majistire mai lamba 29, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Talatu Makama.

A jiya Laraba ne dai a ka gurfanar da Yakubu a kotun, inda lauya mai gabatar da ƙara, Barista Garzali Bichi ya roƙi kotu da ta karantowa wanda a ke zargin tuhumar da a ke yi masa.

Bayan kotu ta karanto tuhumar cikin harshen turanci, sai jami’in kotu, Ibrahim Koya ya fassarawa Yakubu, in da shi kuma nan take ya musanta laifin da a ke tuhumar shi da shi, wanda ya saɓa da sashe na 221 na kundin dokokin kaifuka na Jihar Kano, wanda a ke kira ‘penal code’ a turance.

Advertisement

Tuni dai Mai Shari’a Talatu Makama ta bada umarnin aikewa da wanda a ke zargin zuwa gidan yari har sai ranar 24 ga watan Febrairu sannan za a sake gabatar da shi a gaban kotun.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *