News
TUC ta gindayawa gwamnatin Najeriya sharudda kan shirin cire tallafin mai
Daga Yasir sani Abdullah
Kungiyar Kwadagon Najeriya ta TUC ta gindayawa gwamnatin Najeriya sharuddan da ta ce dole ta kiyaye kafin aiwatar da shirinta na cire tallafin man fetur nan da ‘yan watanni.
Bayan taron da ta yi a ranar Asabar ne dai TUC ta zayyana tabbatar da gyara dukkanin matatun man Najeriya da fara aikinsu, da kuma wadata al’ummar kasar da abinci kan farashi mai rahusa da samar da ababen more rayuwa, a matsayin sharuddan da ta gindayawa gwamnatin kasar kafin ta amince da shirinta na cira tallafin man fetur.
A cikin watan Nuwamban da ya gabata, Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed, ta bayyana shirin cire tallafin man fetur, wanda ta ce za a maye gurbinsa da bayar da tallafin sufuri na naira dubu biyar ga masu karamin karfi akalla miliyan 40, domin rage musu radadin tasirin da matakin zai haifar.
Batun cire tallafin mai a Najeriya ya sake tasowa a ne, bayan da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, ya baiwa gwamnatin kasar shawarar cire tallafin, domin karkata kudaden zuwa ayyukan raya kasa, inda shugaban kamfanin mai na NNPC Mele Kyari ya ce farashin man fetur din na iya haura naira N300 kan lita guda daga shekarar nan da muke ta 2021.