News
An bayyana karatun Alqur ani me girma dayin amfani dashi a matsayin wata hanya ta tsira anan duniya da ma gobe kiyama.
Abdulkadir Muhammad Sani
Wannan bayani Ya fito ne ta bakin shigaban makarantar Adam Mai Agogo dake sharada a karamar hukumar birni, Mal. Yahya Muhammad Adam, a yayin saukar karatun Alqur ani me girma, Karo na 11 na dalibai 46.
Inda Kuma yayi Kira ga iyayen yara Dasu basu goyon baya Dan ganin ankai makrantar zuwa babban mataki.
A nasa jawabin Alhaji Ahmad Tijjani Adam Mai Agogo, wanda ya wakilci shugaban kungiyar iyayen yara wato PTA na makarantar, Kira yayi ga mahukunta da Masu hannu da shuni, dasu kaima makrantar dauki na ajujuwa da sauransu.