Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da shirinta na janye tallafin man fetur har sai baba ta gani.
A baya dai gwamnatin ta shirya janye biyan kuɗaɗen tallafin man fetur ɗin a watan Yulin shekarar nan ta 2022.
Ministar kuɗi da kasafi da tsare-tsare ta Najeriya Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan a wani taro da aka yi a majalisar dokoki a yau Litinin a Abuja.
Taron ya samu halartar shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da ƙaramin ministan man fetur Timipre Sylva, da kuma shugaban kamfanin mai na NNPC Mele Kyari.