News
Kotu ta ba da umarnin kama Diezani mai Bireziyar Zinare
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
A ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da sammacin kamo tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke, wadda ake kyautata zaton tana zaune a kasar Birtaniya.
Mai shari’a Bolaji Olajuwon ya amince da bukatar ne bayan lauyan Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Farouk Abdullah, ya gabatar da bukatar baka.