Connect with us

News

Wani mutum ya rataye kansa a jihar Jigawa

Published

on

FB IMG 16431133954998508
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

Wani mutum mai shekara 25 ya kashe kansa ta hanyar rataya a wani gari da ke karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kakakin ‘yan-sanda a jihar ta Jigawa, ASP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce, mutumin wanda da farko aka bayar da rahoton batansa, an same shi ya rataye kansa ne a wata bishiya da ke bayan gari a kauyen Zangon Maje na karamar hukumar, inda ya yi amfani da wandonsa a matsayin igiya, a jiya Litinin, 24 ga watan Janairu, 2022.

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar ‘yan-sandan jihar ya ce a ranar Litinin ne Hakimin Kwalam, Alhaji Muttaka Uba ya kira su inda ya sheda musu cewa wani mutum Naziru Badamasi, mai shekara 25 na kauyen Tsadawa da ke karamar hukumar Taura, wanda kuma yake da tabin hankali, ya bata bayan ya bar gida a ranar da misalin karfe goma sha biyu da rabi na rana.

ASP Shiisu ya ce daga bisani ne aka gano mutumin ya rataye kansa a bayan garin kauyen Zangon Maje, wanda shi ma a yankin wannan karamar hukuma yake.

Kakakin ya ce da samun wannan labari aka tura jami’an ‘yan-sanda suka je wurin, inda suka dauko gawar suka kai ta babban asibitin Ringim, inda likita ya tabbatar da cewa mutumin ya rasu.

Advertisement

Jami’in ya kara da cewa daga baya ne suka mika wa ‘yan uwan mamacin gawar domin yi masa jana’iza kasancewar binciken farko-farko da suka yi ya nuna cewa ba wani zargi da ake na wata makarkashiya kan mutuwar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *