News
Babban taro: APC ta musanta raba muƙamai na shiyya-shiyya
Daga muhammad muhammad zahraddin
Jam’iyyar APC ta nesanta kanta daga wani jerin sunaye da ke ta zagaye da ta ya bada bayanin yadda jam’iyar ta raba muƙamai shiyya-shiyya kuma a ka ce Shugaban Riƙon Ƙwarya na jam’iyar, Mai Maka Buni ne ya sanar da shi.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Mamman Mohammed ya sanya wa hannu a yau Laraba.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “An janyo hankalin Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Rikon Ƙwarya na Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ga kafafen yada labarai tare da zargin cewa shi ne ya sanar da raba ofisoshin a shiyya-shiyya .
“Ya musanta jerin sunayen da ake ta yaɗawa, yana mai cewa, karya ne, marar tushe, yaudara ce kuma ba shi da alaka da shi.”
Buni ya ce jam’iyyar APC ba ta ɗau wani mataki a ko wane fanni kan wani abu da ya shafi shiyyar ofisoshin ba.
Ya ce, “ kawai na tunanin marubucin ne da ba shi da alaka da Shugaban jam’iyyar da ma jam’iyyar baki ɗaya.
“Ana kira ga jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da ake zargin cewa yaudara ce kuma gaba daya karya ce.”
Shugaban ya bukaci ‘yan jarida da su bijirewa labaran da ba a tabbatar da su ba, da kuma jita-jita, da kuma tabbatar da duk wani abu da ya shafi jam’iyyar, tare da yin alkawarin cewa kofofin jam’iyyar a bude suke don neman bayanai.