News
Mu na da man fetur isashshe domin amfanin ƴan ƙasa — NNPC
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa, yana da isashshen man fetur don biyan bukatun ‘yan Najeriya.
Garba Muhammad, mai magana da yawun NNPC ne ya bayar da wannan tabbacin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba.
Muhammad ya shawarci jama’a da kada su riƙa sayen man fetur don gudun ƙarancin sa kuma su yi watsi da duk wata jita-jita da ke nuna akasin haka.
“La’akari da dokokin da ake da su a kasar, kamfanin NNPC ya himmatu matuka wajen tabbatar da tsaron makamashin kasar,” in ji Shugaban NNPC.