News
Gudun wuce sa’a ya haddasa mummunan haɗari a Kano
Daga muhammad muhammad zahraddin
Ana fargabar rasa ran wani direban mota sakamakon gudun wuce Sa’a da yake yi a safiyar ranar Asabar.
Haɗarin ya faru ne a titin Goron Dutse sakamakon taho mu gama da motoci biyu suka yi.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa guda daga cikin motar ita ce ta ke gudun wuce Sa’a wanda hakan ya sa ta je ta bige ɗaya motar da ke gabanta.
Sai dai tuni jami’an ƴan sanda da ke sintiri a yankin suka kai ɗauki tare da gaggawar kwashe waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake duban tsaftar muhalli a yau Asabar, wanda hakan ya tilastawa tawagar tsaftar muhalli ta kai ɗaukin gaggawa wajen ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim getso.