News
Rage kudin Siminti Zai Sa Gidaje Suyi Arha: CBN Ta Roki A Sassautawa ‘Yan Kasa

Halin yanzu ana sayar da buhun siminti kusan N5000
Babban bankin Kasa Ya Bukaci Kamfanin BUA, Da Dangote Da Su Rage Farashin Siminti da yake neman gagarar ‘yan Najeriya
Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya bukaci masu kera siminti a kasar da su yi la’akari da faduwar farashin kayayyakin.
A cewar Emefiele, ya kamata kamfanonin kera kayayyakin su yi kokarin rage farashin kayayyakin gine-gine a kasar nan, domin samun saukin gidaje.
Emefiele ya yi wannan roko ne ranar Alhamis a wajen kaddamar da sabon kamfanin siminti na BUA da shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar a Sokoto.
Don haka ya yi kira ga kamfanonin kera Siminti da su mai da hankali sosai wajen biyan bukatun cikin gida a fannin samar da ababen more rayuwa domin rage farashin siminti.