News
Koriya Ta Arewa ta harba makami mai linzami mafi girma cikin shekaru biyar
Daga
muhammad muhammad zahraddin
Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami a gabar tekun gabashin kasar, gwajin makami mai linzami na bakwai cikin wata guda kuma mafi girma cikin shekaru biyar.
Gwamnatin Japan ta ce makamin ya yi tafiya mai tsirin kilomita dubu biyu kafin ya gangaro, ya fada tekun Japan mai nisan kilomita dari takwas daga wurin harba shi.
Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya kira taron gaggawa na kwmitin tsaron kasar na farko cikin shekara guda.
Shugaban kasar, Kim Jong Un, ya yi kira ga sojoji da su hanzarta bunkasa fasaharsu da karfinsu, tare da yin watsi da kiran da Amurka ta yi na tattaunawa kan kawar da makaman nukiliya.