Connect with us

News

Atiku Ya yi Tsufa da Shugabancin Najeriya – Gwamnan Bauchi

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani abdullahi 

 

 

Advertisement

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce ya fadawa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar cewa ya yi tsufa da rike shugabancin Najeriya.

Ya fadi hakan ne yayin da ya karbi rahoto daga kwamitin shawara akan takarar shi ta shugabancin kasa inda ya ce Atiku zai yi saurin gajiya da aikin kasar shi.

Gwamnan ya ce idan Al’ummar Nigeriya suna so Atiku ya zama shugaban kasa zai goya masa baya domin shi baya matukar bukatar babban ofishin a kasar nan.

Advertisement

“Babu amfani mu zama masu hadama” dan takarar Shugabancin kasar ya fada.

“Hakika zama na Shugaban kasa ba zai jawo rarrabuwar kai ba, zaku ga a lokacin da yayana Mal Adamu yana Zagayawa mun gayyaci babban dattijo wanda muke matukar girmamawa wazirin Adamawa Atiku Abubakar muka sakawa wata hanya da suna da sunan sa.

“Mun gayyace shi Bauchi kuma mun tattauna nake fada masa a wannan takarar nasan shine babba kuma ya chanchanta Amma shekarun sa zasu saka yayi saurin gajiya kuma ya wahaltawa Nigeriya.

Advertisement

“Ya kyale kannin sa ya zama ya wakilce shi ba wai ya dauke haka nan ba.

“Amma idan Al’ummar Nigeriya sun fi bukatar sa zan bashi goyon baya kuma ba wai na damu da takarar bane kuma a ‘yan Nigeriya har dani, kuma duk abin da yake so zanyi, wannan shine yarjejeniyar mu, ina matukar girmama shi.

Atiku shine dan takarar Jam’iyyar PDP a shekarar 2019 har yanzu bai nuna sha’awar sa na tsayawa takarar shekarar 2023.

Advertisement

Tsohon Ciyaman din Sadarwa na Daar a satin da ya wuce Ya ce ko da an zabi Atiku a matsayin Shugaban kasa a shekarar 2023 zai yi aiki a zango daya ne.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *