News
AU ta dakatar da Burkina Faso bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi
Daga Yasir sani abdullahi
Ƙungiyar Haɗin kan Afirka, AU, ta sanar da cewa ta dakatar da Burkina Faso da ga dukkan al’amuran ta sakamakon juyin mulkin da sojoji su ka yi a kasar.
AU ta ce dakatarwar za ta ɗora har sai an dawo da bin kundin tsarin mulki yadda ya dace.
Tuni dama a ka dakatar da Burkina Faso da ga ɓangaren yammacin Afirka, Kungiyar Haɗin kan Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka na Kudu, ECOWAS.
ECOWAS za ta tura jagorori tare da na Kungiyar Hadin kan Nahiyar Turai, EU domin ziyara zuwa Burkina Faso, su kuma gana da jagororin juyin mulkin don tattauna mataki na gaba.