News
Gwamnatin tarayya zata samar da abinci kyauta ga yaran da ba sa zuwa makaranta – Sadiya
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Manistar jinkai Sadiya Kuma shugabar Kwamitin kula da harkokin makarantu na kasa ta ce za a samar da abinci kyauta ga yaran da ba su zuwa makaranta, Sadiya ta kara da cewa za a ba wa iyayen irin wadannan yaran tallafin kudi a lokacin da ake ilmantar da yaran
Ta bayyana haka ne a wajen taro na biyar na kungiyar Technical Working Group of the Alternate School Steering Committee da aka gudanar a ranar Litinin a dakin taro na Treasury da ke Abuja.