News
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tseratar da mutane 113 daga Gidan Marin da yake ba bisa Ka’ida ba.

Daga Maryam bashir musa
Ma’aikatan Hukumar ‘yan sandan ta Kano sun tseratar da mutane dari da sha Uku 113 rufe a wani daki, mutanen da aka rufe sun samu ‘yanci a yau talata bayan kai hari da Hukumar ‘yan sanda tayi zuwa gidan marin da yake ba bisa Ka’ida ba a Na’ibawa ‘Yan Lemo a karamar Hukumar Kumbotso.
‘Yan sandan sun kai farmakin ne bayan rahoton da suka samu daga mutane goma da suka gudo daga gidan marin.
Mai magana da yawun rudunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa a zantawa dashi yace yace “Musa Safiyanu mai shekaru 55 mazaunin Unguwar Na’ibawa ‘yan lemo karamar Hukunar kumbotso yana tafiyar da Gidan Marin ne ba bisa Ka’ida ba ana azabtarda mutane wajen saka musu sarka kuma a rufe su a daki.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa yace rundunar ‘yan sandan ta bawa ma’aikatan ta umarnin gudanar da bincike inda suka shiga aiki cikin gaggawa, sun gano daya daga cikin wanda aka rufe mai suna Aminu Ado dan Na’ibawa ya sha azaba har sai da ya mutu a hannun wani mai suna Abdulladif Musa mazaunin unguwar Wailari a ranar Asabar.
An kama mutane 6 da ake zargi, a yayin bincikar wandanda ake zargi sun bayyana cewa gidan marin ya fi shekara goma suna gudanar dashi duk da cewa gwamnati ta haramta.
Mal Kiyawa yace wasu daga wanda abin ya faru da su daure suke cikin Sarka, suna dauke da rauni Amma an kai su Asibitin Murtala domin basu taimako sannan an Mika su ga gwamnati.
Ya tabbatarwa da mutanen Jahar Kano za a hukunta wandanda aka kama da zarar Hukumar ‘Yan Sanda ta kammala binciken ta.