News
Ya Kamata Matasa Su Shiga Siyasar Jam’iyya inji – Comrade Maihula
daga Muhammad Muhammad zahraddini
An yi kira ga matasa da su shiga duk wani abu da zai daukaka da bunkasa rayuwarsu tareda kawo habakar tattalin arzuki a Nigeria.
Comrade Muhammad Dahiru Maihula, Dan Jarida a Kano ya bayyana haka jim kadan yayin zantawa da msnema labarai a taron matasa da aka gudanar a garin Kano.p
Dahiru Maihula Ya ce lokaci ya yi da ya kamata a matasa su tsunduma cikin harkokin siyasar jam’iyya, da kuma tsarin zabe mai zuwa a shekarar 2023.
Zaku iya tuna cewa dokar ta ‘Not too young to takasa’ ta kasance. ya zama doka, don ba da dama ga tsararraki zuwa su shiga cikin tsarin domin a dama da matasa.