Connect with us

News

DURƘUSHEWAR AREWA: Boko Haram sun janyo asarar dala biliyan 6.9 a Arewa maso Gabas – Gwamna Zulum

Published

on

images 68 1
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum ya ce aƙalla an yi asarar dala biliyan 6.9 sakamakon bala’in Boko Haram a Arewa maso Gabas, a cikin shekaru 13.

Zulum ya bayyana haka a Abuja a ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana gaban Tawagar Jami’an Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa.

Gwamnan ya shaida masu a taron wanda ake gayyatar manya daban-daban a kowane mako cewa, hare-haren ta’addancin ya haifar da ƙuncin talauci, shiga ƙangin mummunar rayuwa da sauran manya da ƙananan matsalolin da al’ummar yankin su ka afka.

Advertisement

“Boko Haram sun haddasa mummunan bala’in gudun hijira da lalata gidaje, ƙauyuka da garuruwa, tare da asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi, haddasa fatara da talauci da kuma illata tattalin arzikin yankin.” Inji Zulum.

“Amma duk da haka, sakamakon ƙoƙarin dawo da zaman lafiya na Bankin Duniya, Kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya su ka yi, ya nuna cewa aƙalla yankin Arewa maso Gabas ya yi asarar dala biliyan 6.9 sakamakon ‘yan ta’adda. Daga cikin wannan ɗimbin asarar kuwa Barno ce ta ɗibga kashi 2 bisa 3 na asarar gaba ɗaya.

“Yan ta’adda sun lalata kimanin abubuwan makarantu 5000 a faɗin Jihar Barno, kuma sun lalata gine-ginen gwamnati za su kai 800, ciki har da ginin sakateriyar ƙananan hukumomi, gidajen kurkuku, gidajen sarakuna da sauran su.”

Advertisement

Zulum ya ce sun lalata hanyoyin bada wutar lantarki za su kai 7130, kuma sun lalata wuraren samar da ruwa kusan 1600.

“Boko Haram sun haddasa samar da mata 49,311 da suka rasa mazajen su. Sai kuma marayun da su ka rasa iyayen su har 49,917. Waɗannan ƙididdigar da gwamnati ta yi ce.” Inji Zulum.

Zulum ya ce a yanzu ana samun nasarar daƙile ‘yan ta’adda. “Kuma babban dalilin samun wannan nasara a yanzu, shi ne ban taɓa zuwa neman ganawa da Shugaban Ƙasa ba, aka hana ni ganin sa ko da sau ɗaya.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *