News
Kotu ta yanke wa mata shekara 9 a gidan yari sakamakon yin garkuwa da yarinya ƴar shekara 3 a Kano
Daga yasir sani abdullahi
Babbar Kotu a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Maryam Sabo a jiya Alhamis ta yankewa wata mata mai suna Sadiya Ahmadu, ƴar shekar 27 hukuncin ɗaurin shekara 9 a gidan yari da Kuma aiki mai wahala bisa laifin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 3.
A cewar takardar tuhumar da lauyan masu shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, an gurfanar da Sadiya bisa tuhuma ɗaya, ita ce, satar mutane.
” Sadiya Adamu ta Titin Badaru, Unguwar Gayawa,, Kano a ranar 22 ga Maris, 2018 da misalin ƙarfe 11 a Gayawa ta yi garkuwa da wata yarinya, Khadija Nura, ƴar shekara 3 da haihuwa da take hannun iyayenta.
Mai gabatar da ƙara ya sanar da kotu cewa, wacce ake ƙara ta buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 1 daga mahaifin Khadija.
Domin tabbatar da shaida, lauyan masu gabatar da ƙara, ya kira iyayen wacce abin ya shafa, inda su ka ba da shaida yadda a kan wacce ake ƙara ta yi garkuwa da ƴarsu.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa tun da fari, a lokacin shari’ar, shaidun masu gabatar da ƙara sun bayyana yadda Sadiya ta yi garkuwa da Khadija daga Gayawa da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano, aka kai ta ƙauyen Karaɗuwa da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Lauyan mai bada kariya, Barista Y.S. Gama, ya gabatar da Sadiya wadda ta kare kanta.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Maryam Sabo ta tabbatar da cewa Lauyan masu shigar da ƙara, Barista M.M Farokh ya gabatar da gamsassun hujjoji waɗanda su ka tabbatar Sadiya ta yi garkuwa da yarinyar.
Mai Shari’ar ta yankewa sadiya hukuncin ɗaurin shekaru 9 a gidan yari tare da yin aiki mai wahala.
Haka-zalika mai shari’ar ta umarci mai laifin da ta biya tarar Naira 200,000 ko kuma ta yi shekara ɗaya a gidan gyaran hali.
Ta kuma ba da umarnin a fara yanke hukuncin daga ranar da aka kama ta da kuma tsare ta a gidan gyaran hali.