News
Abubuwan da ke jawo rushewar ginshikan gina iyali da al’umma
Daga kabiru basiru fulatan
Abubuwa na tashin hankali suna ta faruwa a kewayenmu wadanda idan aka bibiyi silarsu za a ga cewa ginshikan tsarin gina iyali da al’umma ne ke ta rushewa.
Misali, tun a cikin gidanka ka tara iyalai amma ka kasa tsayar da adalci, idan matarka fiye da daya ne kiri-kiri kake zaluntar sauran kana fifita guda.
Wani ma idan dayar yake da ita sam ya gaza yi mata adalcin da addininsa ya shimfida.
‘Ya’yanka ka tara su ka gaza sauke nauyinsu, ba arabi ba boko ba tarbiyya ba sauke babban hakkin ciyarwa da wajen zama.
Ke kuma a naki bangaren kin kasa zama da kishiyoyinki lafiya, ba ki da aiki sai tunanin cutar da su. Daga ka ji kishiya ta kwarawa kishiyarta ruwan zafi, sai ka ji an ce ta yi wa ‘ya’yan miji mugunta wani sa’in har su mutu.
A wasu gidajen kuma, tarbiyyar ta rushe ne tun daga kan maigida da matansa, har ƴaƴa su gani su ɗauka.
A misali, akwai gidajen da idan aka fara faɗa kai ka ce sansanin yaƙi ne, miji ya lakaɗawa mata dukan tsiya a gaban ƴaƴanta, ko kuma ita ta daddage ta cakumi mijinta tana masa tijara da ruwan ashariya. Shi kenan ƴaƴa sai su yi haddar hakan tamkar karatu.
A waje, mun ƙi zama lafiya da maƙwabtanmu, duk hassada ta rufe wa mutane ido ban da son cuta da zalinci da son duniya ba a komai.
A titi yaro ya daina girmama na gaba da darajta shi, babba ya daina tausayi da nuna wa yara ƙauna. Tsoho ba a bakin komai yake ba, yara na iya ruƙa shi da ball kuma ba sannu, ba yi haƙuri.
A kasuwanni da wuraren aiki duk mugunta ta mana katutu, daga me tauye mudu sai mai son ganin bayan runfar maƙwabcinsa ko abokin aikinsa duk don neman duniya.
Mugayen halaye dai ga su nan birjik da suka sa har muka zo matsayin da za a ce malami da ya fi kowa kusanci da yaro bayan iyayensa zai iya cutar da shi duk da amanar da aka ba shi.
Farfesa Nazifi Darma ya kara wasu abubuwan da yake ganin sun ƙara damalmala wannan matsala a cikin wannan bidiyon.
Idan muna son ganin da kyau, to dole sai mun yi da kyau. Don haka ne ma Farfesa Darma ya taya mu lalubo mafita:
Kar mu manta, muhimman abubuwan da za mu rike su ne riƙo da gaskiya da wanzar da ita, amana, kyautatawa da kuma cire kwaɗayi. Wadannan kadai idan muka rike za mu ga sauyi a al’amuranmu.