Connect with us

News

Ni zan buɗewa matasa hanya a dama da su a siyasa — Ɗan takarar Shugaban Matasa na APC

Published

on

FB IMG 16441432898496212
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini 

 

 

Advertisement

Aliyu Muhammed Manzo, wani matashi ɗan takarar muƙamin Shugaban Matasa na Jam’iyar APC na ƙasa, ya bugi ƙirji cewa shi ne zai buɗewa matasan Nijeriya hanya su shiga siyasa a dama da su a ƙasar nan.

A wata tattaunawa da ya yi da Daily Nigerian Hausa a Kano a yau Lahadi, Manzo, ɗan shekara 27 da haihuwa ya ce ya fito takarar ne domin ya zaburar da ƴan uwansa matasa su ma su shiga siyasa su yi kane-kane.

A cewar sa, idan ya zama Shugaban Matasa na APC, zai yi iya ƙoƙarin sa ya ga ya ƙwatarwa matasa, musamman ƴan dangwale haƙƙin su.

Advertisement

Ya ce “na fahimci matasa, musamman ƴan dangwale ba sa samun cikakkiyar damar da ya kamata su samu a siyasa. Su su ke yin zaɓe, su dangwalawa ƴan siyasa kuri’a, amma da ga ƙarshe, su a ke ajiye wa a gefe.

“To in dai na ci zaɓen Shugaban Matasan jam’iya ta APC, zan tabbatar na kwatowa waɗannan matasa ƴancin su a ko ina a faɗin ƙasar nan. Su su ke shan wahala amma kuma sai a manta da su,” in ji shi.

Manzo, wanda ya fito da ga Jihar Kano, ya ce dokar nan ta shigar da matasa harkokin mulki, ‘Not Too Young To Rule’ da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu ita ce ta zaburar da shi ya fito takarar shugaban matasa na APC.

Advertisement

A cewar sa, matasa su na da haƙƙi da dama da za su ne mi ko wanne irin matsayi na mulki a ƙasar nan ba tare da kuɗi ko sanin wani babba a ƙasar ba.

“Ba maganar kuɗi a ke yi ba, magana a ke yi ta jajircewa da dagewa a cimma manufa. Ba wai sai ka na da kuɗi za ka shiga siyasa ba. Ni ba mai kuɗi ba ne, amma sabo da na jajirce, yau gashi ni na ke sa ran ma zan lashe zaɓen.

“Sabo da haka na zama mai buɗewa matasa hanya su shiga a dama da su a siyasa a ƙasar nan,” in ji shi.

Advertisement

Manzo ya ƙara da cewa shigar matasa APC zai ƙarawa jam’iyar farin jini da kwarjini, inda ya nuna cewa shi yanzu ya zaburar da matasa, ya kamata su tashi tsaye su ma su bi sawunsa.

A cewar Manzo, shi ne matashi na farko da ya nuna sha’awar tsayawa takarar Shugaban Matasa a jam’iya mai mulki ta APC a faɗin Nijeriya gaba ɗaya, inda ya nuna yaƙinin cewa shi zai lashe zaɓen.

“Ai ni gani na nake ma ga ni a kan kujerar. Dama ni na fara fitowa na nemi wannan matsayin kuma da ga bisani saura su ka biyo baya na.

Advertisement

“Amma in sha Allah ni zan lashe zaɓen a babban taron APC da za a yi a watan nan na Febrairu,”

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *