News
Akwai yiwuwar kammala aikin layin dogo daga Kaduna zuwa Kano daga nan zuwa Mayun 2023: Inji Ministan sufuri, Rotimi Amaechi

Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Ministan Sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya bayyana cewa suna da niyyar kammala shimfiɗa titin layin dogo, wanda ta taso daga Kano zuwa Kaduna daga nan zuwa watan Mayu na 2023.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai rangadin duba aikin, don ganin yadda aikin yake tafiya.
A ƙarshen makon da ya gabata ne dai ministan ya bayyana yadda rashin kuɗi zai iya kawo tangarɗa a aikin, wanda kalaman nasa ba su yi wa da yawa daga cikin al’ummomin yankin Arewa daɗi ba.
Jama’a dai sun zuba ido su ga ko gwamnatin za ta sa himma wajen kammala wannan aiki, kamar yadda ta kammala wasu muhimman ayyuka a wasu sassa na ƙasar nan.