Rashin amfanar girbi da ƙarancin abinci na tursasa wa iyalai barin gidajensu a cewar WFP, kuma ana buƙatar taimakon gaggawa don kare afkawa cikin bala’i.
Shekara uku aka yi a jere ba a samun damuna mai albarka – kuma farin na ci gaba.
Amfanin gona na ta lalace, dabbobi na ta mutuwa sannan mutum miliyan 13 a Habasha da Somaliya da Kenya na cikin yunwa.
Kayayyakin abinci na ta tsada, kuma rashin samun amfanin gona sosai ya sa babu ayyukan yi a bangaren noma, wanda hakan ya sa iyali ke shiga cikin matsi wajen ciyar da kansu.
WFP ta ce idan har ba a samu taimako ba to za a faɗa cikin bala’in jin ƙan da ake gudu.
WFP ta ce tana neman taimakon dala miliyan 327 don magance farin – wajen samar da abinci da kuɗaɗe a tsakanin al’ummun da abin ke shafa.