News
Gurbataccen man fetur: IPMAN ta bai wa ƴan ƙasa haƙuri
Daga kabiru basiru fulatan
Ƙungiyar Ƴan kasuwar man fetur Masu Zaman Kansu, IPMAN, ta baiwa matuƙa ababan hawa haƙuri bisa siyar musu da gurbataccen man fetur.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa wani ɗan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida mata cewa kamfanin NNPC ne ya yi odar man fetur ɗin da ke ɗauke da sinadarin sulphur da ya wuce kima har lita miliyan 100 cikin ƙasar nan.
Tuni masu ababan hawa su ka fara ƙorafin cewa injinansu sun lalace, musamman a Legas da Abuja sakamakon amfani da gurbataccen man fetur ɗin.
Ya ƙara da cewa tuni ma yanzu haka akwai lita miliyan 100 na man da a ka rarraba a gidajen mai a faɗin ƙasar nan.
Sai dai kuma a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a jiya Talata, Shugaban IPMAN, reshen Jihar Kano, Bashir Dan-Mallam, ya ce dole ne ƙungiyar ta bada haƙuri sabo da ta fahimci ƴan ƙasa sun sayi gurbataccen man da mambobinta ta su ka siyo a defo ɗin Legas, Warri da sauran su.
Ya ce mambobin IPMAN ɗin sun sayo man ne ba tare da sun san cewa gurbatacce ba ne.
Ya zargi jami’an gwamnati, waɗanda su ke aiki a ɗakin gwaje-gwajen ingancin mai da sakaci a bisa ƙin sanar da IPMAN cewa man gurbatacce ne.
“ƴan ƙungiyar mu sun siyo man a defo ɗin Legas z Warri da sauran gurare ba tare da sanin gurbatacce ba ne har sai bayan sun juye shi a gidajen man su,” in ji Dan-Mallam.
Ya kuma baiyana cewa tuni IPMAN ɗin ta tuntuɓi Manajan-Daraktan Kasuwancin Man Fetur na NNPC, Isiyaku Abdullahi, inda Dan-Mallam ɗin ya ƙara da cewa tuni Manajan ya baiwa ƴan ƙungiyar umarnin su dawo da man da su ka siya.
Dan-Mallam ya tabbatar da cewa IPMAN za ta haɗa kai da NNPC domin gujewa sake faruwar hakan.