Connect with us

News

Yan sandan Kanada sun fara kama masu zanga-zangar dokar korona

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

Kungiyoyin ‘yan kasuwa 60 na Kanada da Amurka sun yi kiran a kawo karshen zanga-zangar da ta haddasa babbar hanyar da ta hada kasashen biyu wajen fuskar kasuwanci da masu zanga-zanga suka rufe.

‘Yan sanda sun fara kama masu zanga-zangar yayin da kashi 25 cikin 100 na motocin da ke cikin cunkoson ababen hawa ke ɗauke da yara ƙanana a cikinsu.

Advertisement

Da take magana da BBC, mataimakiyar magajin garin Ottawa Laura Dudas ta bayyana matakin da hukumomi ke dauka.

“Shugaban ‘yan sandan Ottawa ya bayyana karara muna bukatar karin jami’an tsaro, muna rokon gwamnatin tarayya ta kawo mana ɗaukin ‘yan sanda 18,000 domin shawo kan matsalar masu zanga-zangar nan,” in ji ta.

Lamarin ya fara ne tun ranar 9 ga watan Janairu lokacin da matuƙa manyan motocin suka fara nuna ɓacin rai game da dokar da ta tilasta musu yin rigakafin korona kafin su tsallaka iyakar Amurka da Kanada.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *