Wani rahoton shekara-shekara da ƙwararru a fannin tattalin arziki ke fitarwa ya ce kusan rabin al’ummar duniya ne kadai ke rayuwa karkashin mulkin dimokuradiyya.
Sai dai sun ɗora alhakin hakan ga annobar korona, wadda ta sanya aka samu mafi kankantar adadi tun da suka fara binciken a shekarar 2006.
Ɓarkewar annobar ta kara bai wa shugabannin da ke son mulki ci gaba da zama a kan mulki.
Binciken ya nuna cewa fiye da kashi 1 cikin 3 na al’ummar duniya na karkashin mulkin danniya, yawancinsu a China.
Kasashen Norway da New Zealand da Finland na sahun gaba a ingantacciyar dimokuradiyya, yayin da Koriya ta Arewa da Myanmar da Afghanistan ke sahun baya.