
Wata mota ta tsunduma tafki, bayan da ta kwace wa direbanta ta haure gadar Shehu Musa ‘Yar Adu’a da ke kusa da katafaren kantin nan na Jabi Lake Mall da ke unguwar Jabi a cikin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Wasu rahotanni na cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar Juma’ar nan 11 ga watan Fabrairu 2022, sakamakon tsananin gudu da direban motar yake yi ne, wanda hakan ya sa ta kwace masa ta afka tafkin, a lokacin da wata mota ta shiga gabansa, ya yi kokarin kauce mata.

Sai dai rahotanni sun ce direban ya yi sa’a, domin ya tsira da ransa, kuma kadan ya rage motar fara kirar KIA, ba ta nitse cikin ruwan ba.