Connect with us

Politics

Rikicin Masarautu: Gwamnatin Jihar Kano ta Caccaki Kawu Sumaila Da Rufa’i Sani Hanga’ Da Kuma Yan Majalisar NNPP

Published

on

Rikicin masarautu salisu yahya hotoro
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta na Facebook a baya-bayan nan, Salisu Yahaya Hotoro, babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan kafafen sada zumunta, ya soki ‘yan majalisar Dattawan jam’iyyar NNPP kan yadda suka yi shiru game da rikicin da ya barke a masarautar Kano.

Kalaman Hotoro dai ya shafi Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu da kuma Sanata Rufa’i Sani Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya tare da wasu ‘yan majalisar tarayyar  kasa 17 na NNPP.

Advertisement

Wallafar ta Hotoro, wanda aka rubuta da Hausa, an yada shi a shafin sa na Facebook da aka tabbatar ranar Laraba. Ya nuna rashin jin dadinsa da rashin daukar matakin da ‘yan majalisar suka dauka kan lamarin, duk da irin rawar da suke takawa da kuma nauyin da ya rataya a wuyansu.

“Ina magana ne a kan ‘yan majalisar mu 17 da Sanatoci 2 da muka zaba a karkashin tutar jam’iyyar NNPP da ke wakiltar mu a Abuja. Mutane irin su Aliyu Madaki, AJ Kofa, Kawu Sumaila, Sanata Hanga da sauransu, a wannan lokaci ne ya kamata su fito su yi magana a cikin majalisa kan abin da ke faruwa a Kano,” wani bangare na sakon Hotoro Daya rubuta

“Abin takaici, yanzu muna cikin wani yanayi da muke bukatar jin muryoyinsu. Ya kamata su tashi tsaye su jawo hankalin shugaban kasa, da rundunar ‘yan sandan Nijeriya, da shi kansa Sufeto-Janar su ajiye siyasa a gefe su yi abin da ya dace,” Hotoro ya rubuta.

Advertisement

Ya kuma jaddada cewa rigimar da ke faruwa kai tsaye tana shafar mutunci da kimar gwamna, kuma idan aka yi la’akari da martabar Sanatoci da sauran ‘yan majalisar tarayya na NNPP.

Hotoro ya amince da cewa a halin yanzu majalisar na hutu amma ya dage da cewa hakan bai kamata ya hana Sanatocin fadar albarkacin bakinsu ba.

Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa, yana mai ba da shawarar cewa ‘yan majalisar su yi amfani da kafafen yada labarai na kasa da kasa wajen yin Allah wadai da rashin mutunta Kano tare da matsa kaimi a yi taron gaggawa don magance matsalar.

Advertisement

Kalaman Hotoro na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da zaman lafiya da kishin kasa a daidai lokacin da babbar kotun tarayya ke shirin sauraren kararrakin da suka shafi rikicin masarautar Kano.

An yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a Kano ranar Alhamis.

Kiyawa ya nanata kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi tare da gargadi kan duk wani yunkuri na tayar da hankali.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *